17 Afirilu 2021 - 12:43
An Zargi Gwamnatin Kasar Bahrain Da Azabtar Da Fursunoni Fiye Da 3000 Da Take Tsare Da Su

Wani tsohon dan majalisar kasar ta Bahrain Jalaj Feyruz ne ya yi zargin cewa da akwai fursunonin siyasa da su ka kai 3500 wadanda ake azabtar da su a gidajen kurkuku.

ABNA24 : Jalal Fayruz wanda kamfanin dillancin labarun ( Irna) ya yi hira da shi da safiyar yau Asabar, ya ci gaba da cewa; Shekaru 10 sun shude daga fara yunkurin kawo sauyi a kasar Bahrain, amma har yanzu yanayin kasar yana cikin muni.”

Tsohon dan majalisar kasar ta Bahrain ya kuma bayyana cewa; har yanzu mahukuntan kasar suna ci gaba kai wa mutane hari a gidajensu tare da kama su.

Bugu da kari Feyruz ya ce; Har yanzu ana ci gaba da kama masu wallafa ra’ayoyinsu a shafukan sada zumunta.

342/